Kotu ta halalta auren jinsi guda a Amurka

Shugaban Amurka, Barack Obama
Image caption Wannan hukuncin kalubale ne ga kundin tsarin mulkin Amurka

Masu adawa da aure tsakanin mace da mace ko namiji da namiji a Jihar California ta Amurka sun ce za su daukaka kara bayan alkalin wata kotu ya yi watsi da dokar jihar da ta haramta auratayyar jinsi guda.

Su kuwa masu fafutukar kare hakkokin 'yan luwadi da madigo a wajen kotun da ke San Francisco, cike su ke da farin ciki, bayan alkalin ya yanke hukuncin cewa dokar ta Jihar California ta sabawa kundin tsarin mulkin Amurka.

A cewar alkalin, dokar ta tauyewa masu luwadi da madigo 'yancin da suke da shi na yin auratayya kamar sauran mutane.

Kungiyoyin addini wadanda ke goyon bayan haramta aure tsakanin jinsi guda sun ce aure tsakanin mace da namiji kadai ake yinsa.

Wannan hukunci dai kalubale ne ga kundin tsarin mulkin Amurka; hakan kuma na nufin tasirinsa zai kai ko ina a fadin kasar.

Watakila dai sai Kotun Kolin kasar ce za ta yanke hukuncin karshe a kan wannan al'amari.

Hukuncin Kotun Kolin zai game kasar baki daya, amma ba zai hada kan mutanenta ba.

Akasarin Amurkawa dai na adawa da aure tsakanin jinsi guda; hasali ma jihohi biyar ne kacal a kasar suka amince da shi.