Ivory Coast ta ayyana lokacin zabe

Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo
Image caption Kakakin hukumar zaben Ivory Coast ya ce a watan Oktoba ya kamata a yi zabe

Hukumar zaben kasar Ivory Coast ta bayyana lokacin da take ganin ya dace a yi zaben shugaban kasar.

Kakakin hukumar, Bamba Yakouba, ya ce a watan Oktoba mai zuwa ya kamata a yi zaben shugaban kasar.

Sai dai ya ce kafin hakan sai gwamnatin kasar ta cika wasu sharudda.

Shekaru biyar da suka gabata ne dai ya kamata a yi zaben shugaban kasar ta Ivory Coast, amma aka gaza yin hakan.

Kasar ta Ivory Coast dai ta rabe gida biyu a siyasance tun shekarar 2002, bayan 'yan tawaye sun karbe iko da arewacin kasar.