Amurka ta tuhumi wasu da taimakon Al-Shabaab

Kungiyar Al-Shabab
Image caption Kungiyar Al-Shabab

Masu gabatar da kara a Amurka sun tuhumi wasu mutane 14 da zargin taimakawa kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Alshabab a Somaliya.

Daga cikin mutanen da ake zargi, guda 10 sun fito ne daga Minnesota wadanda a kayi amanna sun yi takakkiya ne daga Amerika zuwa Somalia.

Ita dai kungiyar Alshabaab tana gwagwarmaya ne kan gwamnatin Somalia, sannan akwai zargin cewa tana da alaka da kungiyar Alqaeda.

Antoni janar na Amurka Eric Holder ya ce wannan kame zai aika da gargadi mai zafi ga duk wanda ke yunkurin shiga ko kuma bada gudunmuwa ga kungiyar ta al-Shabaab.