Dattijan arewa sun ce a bi a hankali kan tsarin karba-karba

A Nijeriya kungiyar dattawan arewa ta Northern Elders Group dake goyon bayan tsarin karba-karba a kasar, da kuma kishiyarta ta Northern Summit Group dake so a yi watsi da tsarin na karba karba, sun amince kowacce ta ci gaba da neman biyan bukatarta cikin lumana da mutunta juna.

Kungiyoyin sun kuma yi kira ga jam'iyar PDP mai mulkin kasar ta samo hanyar fita daga mahawarar da batun ya jawo ba tare da nuna son kai ba.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne a wajen wani taro da suka yi jiya a Abuja.

Tsarin na karba-karba dai ya jawo takaddama a tsakanin kungiyoyin abinda ake ganin zai iya haddasa rigima idan ba a sha kansa da wuri ba.