Takaddama a kan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Masana kundin tsarin mulkin Najeriya sun ce wajibi ne shugaban kasa ya sa hannu a kan gyaran da majalisun dokoki suka yi

A Najeriya, bisa ga dukkan alamu har yanzu akwai sauran ce-ce-ku-ce dangane da gyaran kundin tsarin mulkin da majalisun dokokin kasar suka kammala.

'Yan majalisun dai sun sauke wajibinsu, to amma tambayar ita ce: shin sauye-sauyen na bukatar sa hannun shugaban kasa kafin a fara aiki da su?

Ya zuwa yanzu dai Shugaba Goodluck Jonathan bai sa hannu a kan sauye-sauyen ba.

Kuma saboda haka ne wadansu mutane, cikin su har da tsohon shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Mista Olisah Agbakoba, suka je kotu inda suke kalubalantar rashin sa hannun shugaban kasar a kan sauye-sauyen.

Barrister Yahaya Mahmood wani lauya ne mai zaman kansa, ya kuma shaidawa BBC cewa rashin sa hannun shugaban kasar a kan sauye-sauyen ka iya tunzura karin wadansu mutanen su shigar da kara a kotu.

“Ya kamata a ba mu doka wadda aka yi ta bisa doka”, inji lauyan.

A cewarsa, sashe na hudu na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ne ya ba majalisun kasar damar yin doka, “sannan sai sashe na hamsin da takwas ya ce…ko wacce doka suka yi dole su kaiwa shugaban kasa ya sa hannu….

“Ina tsammani ba a tunasar da [‘yan majalisun] ba ne cewar shi kanshi Tsarin Mulkin dda muke amfani das hi yanzu dokar kasa ta kawo shi wadda shugaban kasa ya sa hannu”.