Kungiyoyin agaji na cigaba da bayar da tallafi a Pakistan

Wakilin BBC a arewa maso yammacin Pakistan yace kungiyoyin bada agaji na cikin gida na taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa dasu wadanda kuma ake ganin suna da alaka da wasu kungiyoyi masu tada kayar baya.

Miliyoyin mutane ne dai suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan wadanda yanzu haka ke mutakar bukar taimakon gaggawa.

Kawo yanzu dai Hukumomin kasar ta Pakistan dai sunce sun kwashe fiye da mutane dubu dari biyar a yankuna bakwai dake lardin Sindh.

Javed Iqbal,wani jami'i samar da agaji ne dake garin Pahar Pul, a yankin Layyah,ya ce mutane da dama basa son barin dabbobinsu idan aka zo kwashe su.