Yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Pakistan ya karu matuka

Ambaliyar ruwan Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwan Pakistan

Jami'an bada agajin gaggawa a kasar Pakistan sunce, yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a kasar yayi matukar karuwar ban mamaki inda ya linka zuwa mutane miliyan goma sha biyu.

Wakilin BBC a Islamabad ya ce, yanzu haka ruwa ne ke ci gaba ambaliya a lardin Sindh, lamarin da ya sa mutane da dama suka rasa muhallansu.

Shugaban kasar ta Pakistan dai Asif Ali Zardari, yayi ta fuskantar suka a cikin gida saboda shawararsa ta kai ziyara zuwa kasashen turai maimakon komawa gida don sa ido da kansa kan yadda ake tafiyar da ayyukan bada agaji.

Sai dai Shugaba Zardari ya ce Firayim Ministan kasar ya isa ya tafiyar da duk wasu abubuwa da ka iya tasowa.

Ambaliyar ruwan dai na kara kwarara a wasu yankunan kasar Pakistan yayin da ake ci gaba da sheka ruwan sama mai kama da bakin kwarya.

Kogunan da ke Lardin Sindh a tsakiya da kuma kudancin kasar ta Pakistan sun cika sun batse yayin da ruwan ke gangarawa zuwa teku.

Tuni dai aka umurci dubban mutane da al'ummun da ke yankin Kogin Indus a lardin na Sindh su bar gidajensu.

A duk shekara dai a kan samu ambaliyar ruwa a Sindh, amma ba a taba samun ruwa mai yawan da ake zaton za a samu a 'yan sa'o'i masu zuwa ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa a mako gudan da ya gabata mutane dubu da dari shida ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan.

Ta kuma ce ambaliyar ta rutsa da mutane miliyan hudu.

Ruwan dai ya wanke hanyoyi da gadoji, ya kuma rusa dubban daruruwan gidaje.