Fidel Castro ya yi gargadi kan hadarin yakin nukiliya

Fidel Castro

Tsohon shugaban Cuba, Fidel Castro, ya yi gargadi a kan hadarin da ke tattare da yaki da makaman nukiliya.

Ya fadi hakan ne a jawabinsa na farko ga majalisar dokokin Cubar a cikin shekaru hudu.

Mr Castro, wanda ya mika mulki ga kaninsa Raul, bayan da aka yi masa tiyata a ciki a shekara ta 2006, ya yi ikirarin cewa Amurka tana shirin kai hari a kan Iran da Korea ta Kudu.

Amma ya ce shugaba Obama yana da ikon dakatar da hakan.

Ya ce amma in bai hana ba, "To tamkar ya bada umurni ne na kashe daruruwan milyoyin mutane, ciki har da dama daga kasarsa".