Mutane ashirin sun mutu a kasar Iraqi

Image caption Wurin da lamarin ya auku a Basra

Akalla mutane ashirin ne suka halaka sakamakon wasu jerin fashewar abubuwa, a babbar kasuwar birnin Basra dake kudancin Iraqi.

Takamaiman dalilin fashewar abubuwan dai bai samu ba.

Kodayake wasu rahotanni na nuna cewa wani janareta ne ya haddasa alamarin, yayinda wasu kuma ke cewa bam ne da aka dana a gefen titi da wata mota makare da bama bamai suka haddasa lamarin.

Wani dan majalisa Hussein Talib ya dora alhakin fashewar abubuwan akan jamian tsaro.