Libya ta ba Nijar Tallafin Abinci

Image caption wata yarinya wadda ke kokawa dangane da rashin abinci a Nijar

Kasar Libya ta bada tallafin tan dari takwas na abinci da ya hada da gero, dawa, masara, da shinkafa ga jamhuriyar Nijar.

Kasar ta Libya dai ta yunkuro ne domin bada nata gudunmuwa, wajen shawo kan matsalar yunwa da ke addabar wasu yan kasar sama da miliyan bakwai.

Haka zalika kasashen biyu sun kafa wani asusu na dalar miliyan dari domin sanya jari a fannoni daban - daban na bunkasa ci gaban kasashensu.

Kasar Libiyar dai ta ce a shirye take ta tattauna da Nijar, game da sabanin iyakar da ke tsakaninsu.

Kasashen biyu sun amince da haka ne a jiya yayin wata ziyarar aiki da firaministan Libya ya kai a jamhuriyar Nijar.