Shugaban Pakistan yayi fatali da sukar da ake masa

Image caption Wasu daga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Pakistan

Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari, yayi fatali da sukar da ake masa na cewa kamata yayi ya koma kasarsa daga wani dogon tafiyar da yayi zuwa kasashen ketare, domin sanya ido akan aikin bada tallafi ga yan kasar, inda balain ambaliyar ruwa ya shafi mutanen kasar milliyan goma sha biyu.

A hirar da yayi da BBC Mista Zardari ya kare shawarar da ya yanke don zuwa Birtaniya inda ya ce Firaministan Pakistan na sa ido kan yadda ake tafiyar da ayyukan bada agaji a kasar.

An dai tayi wa Mista Zardari kira akan ya soke ziyararsa zuwa Birtaniya domin ya nuna rashin amincewarsa kan kalaman da suka fito daga bakin Firaministan kasar David Cameron., wanda ya zargi Pakistan da gudunar da ayyukan ta'adanci a wasu kasashen ketare. Kuma bayan haka ne mumunnar ambaliyar ruwar ta afka ma kasar wadda ba'a taba fuskantar irin ta ba a shekaru goma da suka gabata.