Jihar Ribas za ta bullo da asibiti cikin jirgin ruwa

Gwamnatin Jihar Ribas dake Kudu Maso Kudancin Najeriya, ta bullo da wani sabon salon amfani da Jiragen Ruwa masu asibitoci a ciki don amfanin al'ummomin da ke Rayuwa a kan Ruwa.

Wannan Yunkuri da Gwamnatin ta yi, a cewar Kwamishin Kiwon Lafiyan Jihar, Doctor Samson Parker, an yi shi ne, sakamakon karancin Dakunnan Shan Magani a kauyukan da ke kan Ruwa.

Da dama daga cikin Alummomin Yankin Naija Delta, suna rayuwarsu ne a cikin Ruwa sakamokon makwabtaka da suka yi da Kogin Atlantika.