An zargi Sudan da hana samar da agaji a Darfur

Image caption Mayakan wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya

Jami'an dake ayyukan jin kai na Majalisar dinkin duniya sun ce, mahukuntan Sudan na hana kungiyoyin bada agaji kai ziyara sansanin yan gudun hijira a yankin Darfur, inda aka tsugunar da mutane fiye da dubu dari wadanda suka rasa matsugunansu.

Offishin Majalisar akan harkokin bada agaji ya ce, an hana su shiga yankin na tsawon kwanaki biyo bayan rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin yan tawaye a sansanin na Kalma a makon jiya.

Mutane da dama ne suka rasu, sakamakon rikicin kuma kakakin wata kungiyar agaji ya ce alamarin ya munana, kuma ana ci gaba da tattaunawa tare da mahukunta kasar, don samun maslaha game da haramcin shiga yankin.