Shugabannin Venezuela da Colombia zasu gana da juna

colombia
Image caption Ministocin harkokon wajen Colombia da kuma Venezuela

Ministocin harkokin wajen Colombia da Venezuela sun yi shelar cewa shugabannin kasashen biyu zasu gana da juna, a gobe a Bogota babban birnin Colombia a wani yunkunin daidaita huldar dake tsakaninsu.

Sanarwar ta zo ne kwana daya bayan sabon shugaban kasar Colombia, Juan Manuel Santos ya nuna alamun a shirye yake ya tattauna da shugaba Hugo Chavez.

Shugaban kasar Venezuela ya yanke duk wata huldar da kasar Colombia makoni biyu da suka gabata, bayan zargin da kasar tayi masa akan cewa yana goyon bayan kungiyar FARC masu ra'ayin sauyi.