Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta raba abinci a Damagaran

A Kalla kimanin yara dubu dari da tamanin da dari takwas da hamsin da bakwai ne da iyayen su ke samun taimakon abinci a jahar Damagaram daga hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya PAM.

Hukumar dai tace tana bada abincin ne ga yaran da iyayen su bayan wani bincike data gudanar mai nunin cewa iyayen na anfani da wannan gari mai gina jiki da ake ba yaran, hakan yasa cutar tamowa na dada samun gidin zama ga yara.

Yanzu haka wata tawaga ta ma'aikatan hukumar tare da rakiyar 'yan jaridu na cikin jahar ta Damagaram dan ganin yanda ake tafiyar da rabon abinci.