'Yan sanda sun harbe dalibi a Maiduguri

Rahotanni da jihar Borno a Najeriya na cewa wani dalibi mai suna Muhammad Musa ya rasa ransa, yayin da wasu daliban biyu suka jikkata a jami'ar Maiduguri.

Hakan ta auku ne sakamakon harbin da 'yansanda suka yi a kofar harabar jami'ar a karshen makon nan.

Wannan kuwa ya faru ne a lokacin da daliban ke fitowa daga harabar makarantar tasu domin tafiya dakunan kwanan su rukunan gidaje na 202 da 303 dake daura da jami'ar, inda aka fara wata tankiya tsakanin wasu dalibai da 'yansandan.

Rundunar 'Yansanda ta jihar Bornon dai ta bayyana cewar tana nan tana gudanar da bincike game da wannan al'amari.