Jam'iyyar NEPU ta cika shekaru sittin da kafuwa

Image caption Najeriya

Jam'iyyar NEPU mai fafutukar samarwa talaka yanci ta gudunar da bikin cika shekaru sistin da kafuwa.

NEPU dai na cikin jam'iyyun siyasar Najeriya a lokacin jamhuriya ta daya.

Koda yake jam'iyyar a yanzu bata, amma har yanzu wasu 'yan siyasa a Arewacin kasar na bugun kirji da akidar da ta kira 'ta fafutukar samarwa talaka 'yanci' daga abinda tace danniyar mahukunta a wancan lokacin.

A yanzu dai babu abinda yan siyasa da dama musamman a Jahohin Kano da Jigawa suka fi kokarin danganta kansu da su kamar jam'iyyar ta NEPU.

Har yanzu dai akwai sauran yan jamiyyar kalilan, wadanda ke raye kuma a jiya sun yi wani bikin cika shekaru sistin da kafuwar jam'iyyar.