Dmitri Medvedev ya kai ziyara Abkhaziya

Shugaba Dmitri Medvedev na Russia, ya kai wata ziyarar ba-zata a Abkhaziya, yankin na kasar Georgia da ya balle.

Wannan ce ziyararsa ta farko zuwa yankin tun bayan da Russiar ta fafata da Georgia a kan ballallen yankin, a wani dan gajeren yaki shekaru biyu baya.

Tuni kuma Russia ta amince da Abkhaziar a matsayin kasa mai 'yancin kanta.

Wakilin BBC ya ce, "Bayan da Shugaba Medvedev ya yi tattaki a bakin Bahar Aswad (ko kuma Bakin Teku), a Sukumi, babban birnin kasar, shugaban ya kare amince da 'yancin kasar da Russia ta yi shekaru biyu baya."