An sami karuwar mutanen dake mutuwa a Afghanistan

Image caption Mayakan Amurka a kasar Afghanistan

Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta wallafa ya ce an samu karuwar yawan fararen hular da rikici ke shafa a Afghanistan a cikin kashin farko na shekarar nan.

Rahoton ya ce hare haren masu tayar da kayar baya sun karu, to amma alhaki kalilan ne dakarun kungiyar tsaro ta NATO ke da shi wajen mutuwar fararen hula.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yawan mutane fararen hular da ke mutuwa ko yin raunuka sakamakon yakin Afghanistan ya karu fiye da a baya.

Rahoton wanda aka fitar a birnin Kabul, ya ce yawan fararen hular da yakin yake shafa ya karu da kashi talatin da daya cikin dari kuma kungiyar Taliban da sauran masu tayar da kayar baya ne ke da alhakin kashe ko raunata rubu'i na wadanda abin ya shafa.

Sai dai wani kakakin 'yan Taliban din ya fadawa BBC cewa akwai kuskure a rahoton na Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa fararen hula 'yan kalilan ne suka hallaka a hare-haren da 'yan Taliban suka kai.

A halin da ake ciki kuma, hukumomin Afghanistan din sun ce faraen hula hudu sun rasa rayikansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Kabul.

Image caption Abaya an sha zargin sojojin tsaro na NATO da laifin kai hari ga fararen hula

'Sun karu da kashi 31 cikin dari'

Da yake jawabi ga manema labarai a Kabul, wakilin Majalisar na musamman a Afghanistan, Staffan Da Mistura ya bayyana cewa:

"Fararen hular da yakin ya shafa sun karu da kashi 31 cikin dari idan aka kwatanta da yawan a daidai wannan lokaci a shekarar 2009".

Wanna yana nufin fararen hula 3,268 ke nan wadanda aka kashe ko aka raunata a watanni shidan da suka gabata.

Rahoton ya bayyana cewa mutane 1,997 ne suka yi raunuka yayinda 1,271 suka rasa rayukansu a watanni shidan da suka gabata.

Rahoton ya kuma bayyana cewa mata da kananan yara ne suka fi jin jiki sakamakon yakin na Afghanistan, inda yawan yaran da bama-bamai suka hallaka ya karu da kashi dari da hamsin da biyar idan aka kwatanta da bara.

Rahoton ya tabbatar da cewa wadannan alkaluman na nuna yawan fararen hula 'yan Afghanistan da yakin ya shafa ne kawai.

Kuma ko da yake rundunonin kasashen waje da ke kasar sun yi kokarin rage yawan fararen hular da suke kashewa-kuma sun yi nasarar ragewar da kashi talatin cikin dari.

Karuwar yawan wadanda yakin ke shafa na nuni da karuwar rashin tsaro a fiye da ko wanne lokaci a tsawon shekaru tara da aka yi ana yakin.