Jama'iyar AC ta yi babban taronta a Ikko

Jam'iyya ta ukku mafi girma a Najeriya, watau Action Congress, ta fara babban taronta na kasa baki daya a birnin ikko.

Masu aiko da rahotanni sun ce Jam'iyyar wadda goyan bayanta ya fi yawa a yankin kudu maso yammacin Nigeria, mai yiwuwa ta kulla wani kawancen tare da Jam'iyyar CPC watau Congress for Progressive Change ta tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan Nigeria, Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

A cikin shekara mai zuwa ne dai zaa gudanar da zaben kasa baki daya a Najeriyar.

Dama dai ita kanta jamiyyar ta AC watau Action Congress an kafa ta ne ta hanyar kawancen wasu jam'iyyun adawa da suka hada da jamiyarr AD, watau Alliance for Democracy a shekara ta 2006.