Majalisa ta amince a baiwa INEC kudi

Shuguban hukumar zaben Nigeria, Farfesa Jega
Image caption Shuguban hukumar zaben Nigeria, Farfesa Jega

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar da shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan, ya gabatar na amincewa da baiwa hukumar zabe ta kasar naira biliyan 89.

Hukumar na son amani da kudaden ne wajen gudanar da zabe a badi.

Hukumar zaben ta ce za ta yi amfani da kudaden wajen yin sabuwar rajistar masu zabe da kuma sayen karin akwatunan zabe da za'a yi amfani da su a zaben na badi.

Tun farko dai hukumar zaben tace, idan har ana son a yi zaben na badi cikin nasara to kuwa sai an ba ta wadannan kudade a kan lokaci.

A yanzu dai ana jiran majalisar wakilai ta kasa ta amince da wannan bukata gabanin a sakarwa hukumar zaben wadannan kudade.