Wasu 'yan arewa sun kulla yarjjeniya da yan kabilar Igbo

Shugaban Jam'iyyar PDP
Image caption Shugaban Jam'iyyar PDP

A Najeriya wata kungiyar dattawa`yan siyasa daga arewacin Njeriya mai suna Northern Elders Political Forum ta kulla wani kawance da wata kungiyar dattawan al`umar Igbo mai suna South-East Political Forum don tabbatar da dorewar tsarin mulkin karba-karba a Najeriya.

Bangarori biyun dai sun amince da za su taimaka wa juna wajen ganin cewa dan arewacin Najeriya ne zai kasance shugaban kasa a zaben badi.

Haka kuma za su goyi bayan juna wajen ganin dan al`ummar Igbo ya kasance shugaban kasa a shekara ta 2015.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na daga cikin wadanda suka halarci taron.