Jam'iyyar CPC ta samu karuwa a Katsina

A yau din nan a Katsina wasu 'yan siyasa daga jam'iyyun PDP da ACN suka sauya sheka zuwa sabuwar jam'iyyar CPC ta Janar Muhammadu Buhari.

Daga cikin wadanda suka sauya shekar har da tsohon Shugaban majalisar wakilai ta Kasa Alhaji Aminu Bello Masari.

An gudanar da bikin karbarsu cikin jam'iyar ta CPC ne a hedkwatar jam'iyyar.

kwanakin baya dai Alhaji Aminu Masari ya kasance a cikin wata kungiyar neman kawo sauyi a jam'iyyar PDP -- PDP Reform Forum abinda ya sa jam'iyyar dakatar da shi, da wasu abokan burminsa, kafin daga bisani ta amince da yin tattaunawa da su.