Mutane 40 sun mutu a Borno

Amai da gudawa ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a jihar borno
Image caption Rashin tsaftataccen ruwan sha na haddasa cutar amai da gudawa

A Najeriya, jami'an lafiya sun ce kimanin mutane arba'in ne suka mutu a jihar Borno,sakamakon cutar amai ga gudawa.

Kazalika sun ce mutane dari da goma sha biyar ne ke kwance rai kwakwai mutu kwakwai sakamakon cutar a kananan hukumomi takwas na jihar.

Annobar mafi muni ta baya bayan nan, ita ce ta yankin Karamar Hukumar birnin Maiduguri da kewaye inda kimanin unguwanni biyar ne dake da yawan jama'a mutane ke rasuwa a gidajen su.

Jami'an kiwon lafiya na kananan hukumomin da annobar ta shafa na bayyana fargabar ci gaba da yaduwar cutar sakamakon rashin isassun wuraren kebe wadanda suka suka kamu.

Sai dai wani likita maisuna Dakta Abba Tijjani ya shaidawa BBC cewa, gwamnati ta ware wurare guda hudu don karbar magunguna.