Kungiyar 'Yan tawayen Uganda na sace mutane

Mista Joseph Kony
Image caption Kungiyar Human Rights Watch ta zargi Mista Kony da sace mutane

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta zargi kungiyar 'yan tawayen Lords Resistance Army dake Uganda da ci gaba da sace daruruwan jama'a.

A wani rahoto da ta fitar,kungiyar ta ce akasarin wadanda Lords Resitance Army din ke sacewa kananan yara ne na yankin tsakiyar Afrika.

Kungiyar ta ce a cikin watanni goma sha takwas da suka gabata, kimanin mutane dari aka sace daga gidajensu a yankunan karkara dake yankin tsakiyar Afrika, da kuma arewacin jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Kungiyar ta ce wasu da suka kubuta cikin mutanen da aka sace sun bayyana cewa, ana tilastawa kananan yara kashe junansu, yayin da kuma ake azabtar da 'yan mata tare da yi musu fyade.

'A kawo karshen cin zarafin'

Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnatin Amurka-da kuma gwamnatocin dake yankin da su kawo karshen cin zarafin da kungiyar ta Lords resistance Army ke yiwa jama'a.