Kuwait za ta saye sabbin makamai daga Amirka

Sojojin Amirka a Kuwait
Image caption Sojojin Amirka a Kuwait

Amurka ta bayyana cewar tana shirin sayarwa Kuwait sabon samfurin naurar dake cafke makamai masu linzami mai suna Patriot.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce Kuwait ce take neman mallakar naurorin kamar gudu dari biyu, kuma cinikin zai kai na fiye da dala miliyan dari tara.

Kasar ta Kuwait dai ta ce tana bukatar wadannan naurori ne domin kariya daga barazanar harin makamai masu linzami da ake iya harbawa daga kasa zuwa sama.