An kaddamar da jam'iyyar Mega party a Nijeria

Taswirar Nijeriya
Image caption Jam'iyyar Mega Progressive Party ta ce za ta karbe iko daga hannun jam'iyar PDP.

A Nijeriya, yau a birnin Lagos, aka kaddamar da sabuwar jam'iyyar Mega Progressive Party.

Jam'iyyar, a karkashin jagorancin Cif Rasheed Adewale Shittabey, ta ce za ta yi gwagwarmaya domin ganin ta karbe iko daga hannun jam'iyar PDP.

Kaddamar da jam'iyyar ya biyo bayan yi ma ta rajista a hukumar zabe ta kasa.

A baya dai wasu fitattun 'yan siyasa a Najeriyar sun sha yunkurin dunkulewa su kafa wata babbar jam'iyyar adawa , domin yin gogayya da jam'iyyar ta PDP mai mulki, amma kuma lamarin ya faskara, sakamakon rashin jituwar da ke kunno kai tsakaninsu.