Indiya ta toshe aika sakonni ta Intanet a wayar Blackberry

Indya ta ce za ta toshe duka hanyoyin aika sakonni ta Intanet daga wayoyin salula na Blackberry, muddin kamfanin dake harhada wayoyin bai warware damuwar da take nunawa ta fuskar tsaro nan da karshen wannan wata ba.

Gwamnatin Indiyan dai tana nuna damuwa ne cewa kungiyoyin masu fafitika za su iya amfani da irin wadannan wayoyin salula wajen shirya kai harin ta'addanci.

Wakilin BBC ya ce sauran kasashe da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Lebanon da kuma Algeria, suma sun bayyana irin wannan damuwa.

Kamfanin dake harhada wayoyin, wanda na Canada ne, yana fuskantar matsin lamba don baiwa gwamnatoci damar shiga shafukan da ake ajiye bayyanan sirri a wayoyin.

Mutane fiye da miliyan daya ne dai ke amfani da wayoyin na Blackberry a kasar ta India.