Hafsan Iraqi ya ce janye sojin Amurka daga kasar zai kasance garaje

Hafsan sojan mafi girman mukami a Iraqi ya nuna shakku dangane da janyewar sojojin Amurka daga Kasar, yana mai cewa sai nan da shekaru da dama masu zuwa ne sojojin na Iraqi za su shiryi karbar ragamar tsaro a kasar.

Laftana Janar Babaker Zebari ya ce shirin Amurka na janye dukan sojojinta dake Iraqi nan da karshen badi, zai kasance wani garaje.

Ya ce," Zaa fara samun matsala ne bayan shekara ta 2011. Me zamu yi a lokacin, idan babu sojojin Amurka? Sai a shekara ta 2020 ne sojojin Iraki za su kasance a shirye".

A jiya dai, Amirka ta dage kan cewa a karshen wannan watan ne za ta janye sojojinta daga filayen daaga a Iraqin, kamar yadda aka tsara.

Haka nan kuma kakakin shugaba Obama, Robert Gibbs ya ce komai shirin janye dukannin sojojin Amurka daga Iraqi na tafiya daidai kamar yadda aka tsara tun farko.