Majalisar wakilai ta amince a baiwa INEC kudi

Majalisar wakilai ta Najeriya ta amince da bukatar da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gabatar na ware wa hukumar zaben kasar sama da naira Biliyan tamanin, domin shirya wa zabe na badi.

A jiya ne dai majalisar ta soma zama kan batun , amma ba ta samu damar cimma yarjejeniya a kan bukatar ba.

Da ma tun a shekaranjiya majalsar dattawa ta kasa ta amince da irin wannan bukata, bayan tafka wata muhara.

Dukkan majalisun biyu dai sun katse hutun da suke yi ne, domin zama kan wannan batu, bayan da shugaban hukumar zaben Farfasa Attahiru Jega yayi kurarin cewa matukar ba amince da wannan bukata ba, to kuwa ba zai bada tabbacin gudanar da sahihin zabe ba a badin ba.