An kammala taron kiyaye zaman lafiya a Kaduna

A Kaduna dake arewacin Najeriya an kammala wani taro na majalisar dinkin duniya da ya duba matsalolin dake tasowa a ayyukan kiyaye zaman lafiya a wasu kasashe na duniya.

Taron ya tattauna ne kan ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasashen da majalisar dinkin duniya ke aika dakaru, domin ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Haka nan kuma taron ya duba wasu sabbin matsalolin dake tasowa da kuma yadda za a magance su.

Najeriya dai na cikin kasashen dake bada karo- karon sojoji domin kiyaye zaman lafiya a kasashe da dama na duniya.