Majalisar tuntubar juna ta amince da sabon tsarin mulki a Nijer

A jamhuriyar Nijer, majalisar tuntubar juna ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

A dazu ne majalisar ta kammala taron da ta shafe kwanaki sha biyar tana gudanarwa.

Haka nan majalisar ta yi na'am da kundin da ke kayyade matsayin adawa da kuma wata doka da ke kayyade tsarin ayyukan jam'iyun siyasa a kasar ta Nijar.

Sai dai ga alamu akwai rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan majalisar a game da wasu ayoyin dokoki, daga ciki har da wadda ta ce sai mutum na da a kalla digiri na farko kafin ya yi takara a zaben shugaban kasar.