Shugaban Pakistan ya ziyarci lardin Sindh

Shugaban Pakistan ya ziyarci lardin Sindh
Image caption Jama'a na ci gaba da fuskantar karancin abinci da sauran kayan agaji

Shugaban Pakistan Asif Ali Zardari ya kai ziyara lardin Sindh domin gane ma idanunsa barnar da ambaliyar ruwa da aka taba yi mafi muni a kasar ta haddasa.

A baya ya fuskanci suka kan yadda ya ki ya katse ziyarar da ya kaa nahiyar Turai, bayan da girman ambaliyar ya bayyana.

A halin da ake ciki, Ministan abinci na Pakistan ya ce akwai yuwuwar cewa mummunar ambaliyar ruwan da ta afka ma kasar ta lalata tarin kayan abincin mai yawa da aka yi tanaji.

Ministan Nazar Muhammad Gondal ya kuma bayyana cewa ana fuskantar matsaloli wajen aikin raba kayan agaji, a sakamakon yadda ambaliyar ruwan ta lalata hanyoyin mota da gadoji.

'barazanar kamuwa da cututtuka'

A kullum wannan bala'i na ambaliyar ruwa kara tsananta ya ke yi. A halin da ke ciki dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce yi kashedin cewa idan ba a samu karin agaji ba mutane za su sake rasa rayukansu.

Image caption Jama'a na kokawar karbar kayan abincin da kungiyoyin agaji ke ba su

Mutane da dama ne dai al'amarin ya rutsa da su kuma suke fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka.

Wani ma'ikacin agaji da ya kai ziyara wasu daga cikin wuraren da abin ya fi tsanani, Habib Malik, ya bayyana irin halin da ya ga wasu sansanonin da mutane suke fakewa.

"A yau tun da dukuduku an tafka ruwa sosai. Na kuma leka wasu daga cikin hemomin da mutane ke kwana-ba zai yiwu a iya barci a ciki ba. Gaba daya wurin tabo ne kuma a jike ya ke. A kwai 'yan gudun hijira dubu shida a wannan sansani. kuma bandaki uku ne kawai"

Wannan dai bala'i ne da ya aukawa bil Adama, a lokaci guda kuma matsala ce ta tattalin arziki.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta kaddamar da daya daga cikin shirye-shiryenta na neman agaji mafi girma ga kasar ta Pakistan don taimakawa mutanen da ke cikin bukata, wadanda ke karuwa.

Tuni dai 'yan siyasar kasar sun fara nunawa juna yatsa suna zargin juna da yin sakaci wajen yin kaykkayawan tanadi don aukuwar ambaliyar.

Shugaba Zardari, wanda bai jima da komawa kasar ba bayan balaguron da ya yi zuwa Burtaniya, ya kai ziyararsa ta farko inda aka yi makwanni biyu ana fafatawa da matslar ta ambaliyar ruwa.