kwamitin zartarwa na PDP ya ce za a cigaba da karba-karba

A Nijeriya, dazu-dazun nan ne kwamitin zartarwar jam`iyyar PDP mai mulkin kasar ya kammala wani zama inda ya amince da cewa jam`iyyar za ta ci gaba da aiki da tsarin karba-karba wajen shugabancin kasar.

Haka kuma ta amince wa shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya tsaya takara idan yana da sha`awar yin hakan a zaben badi.

Batun karba-karbar dai ya haifar da muhawara a Nijeriyar tun wani lokaci da jam`iyyar ta yi wani yunkurin fatali da shi.