Majalisar dokokin Amurka ta amince da sabuwar doka

Majalisar dokokin Amurka ta amince da wata sabuwar doka
Image caption Shugaban Amurka,Barack Obama

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da wata sabuwar doka, wadda za ta bukaci gwamnati ta kashe dala miliyan dari shida don aiwatar da wasu manufofi da zasu karfafa tsaron kasar, a iyakarta da kasar Mexico.

Majalisar ta amince da dokar ne jiya alhamis, abinda ke nufin cewa shugaban kasar Barack Obama zai sanyawa sabuwar dokar hannu a yau Juma'a.

Za a yi amfani da kudin ne domin sayo motoci dubu daya da dari biyar, wadanda za a rika yin sunturi da su a iyakar kasar.

Kazalika, za a biya jami'an hukumar hana fasa-kauri, da sauran ma'aikata don gudanar da ayyukansu.

Shugaba Obama ya ce sabuwar dokar za ta karfafa dangantakar Amurka da kasar Mexico, domin ganin sun yi maganin gungun masu safarar miyagun kwayoyi