Ruwan sama na kawo cikas ga aikin kai agaji a China

Mutane da dama sun halaka sakamakon ambaliyar ruwa a China
Image caption Kasar China na fama da bala'in ambaliyar ruwa

Ruwan sama na kawo cikas ga aikin kai agaji a yankin arewa maso yammacin kasar China inda ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu daya da dari daya.

Masu aikin kai agajin sun ce hakan na dada jefa al'ummar yankin cikin mawuyacin hali.

Ana sa ran za a tafka ruwa a lardin Gansu a yau juma'a.

Sai dai wasu na ganin cewa sare itatuwa barkatai, tare da rashin ingantattun tsare tsaren gidaje a yankunan ne suka yi sanadin wannan bala'i.

Gwamnatin China ta sanar da yin rangwame ga kudin gidajen mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.

Sai dai kwararru na ganin cewa bai kamata mutane su kuma zama a wuraren da abin ya shafa.