EFCC ta gurfanar da Akinbola a kotu

A Nijeiya hukumar EFCC mai yaki da ma su yiwa tattalin arzikin Naijeriya zagon kasa, a yau ta gurfanar da Mr. Erastus Akinbola, tsohon manajan daraktan bankin Intercontinental, a gaban wata babbar kotu da ke a Lagos.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Mr Akingbola a gaban kotun ne bisa zargin bayar da ramcen kimanin naira biliyan 300 ta haramtacciyar hanya.

Sai dai tsohon Manajin Daraktan Bankin na Intercontinental ya musanta zargin da ake ma sa.