Ambaliyar ruwa a jihar Jigawa

Wani da ambaliyar ruwan ta mamaye gidan shi
Image caption Wani da ambaliyar ruwan ta mamaye gidan shi

A jihar Jigawa dake arewacin Najeriya wani gagarumin ruwan sama da akayi a daren ranar Larabar nan ya haddasa ambaliyar ruwa data mamaye wasu unguwanni a garin Jahun hedikwatar karamar hukumar Jahun.

A yanzu dai daruruwan iyalaine wadanda suka tsira daga gidajen nasu suka sami mafaka a gidajen 'yan'uwa yayinda wasunsu kuma suka ci gaba da zama a gidajen nasu duk da mamayewar da ruwan yayiwa ciki da wajen gidajen nasu.

Hukumomin jihar nakai gwauro su kai mari dan shawo kan lamarin.

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa Alhaji Ahmed Mahmud Gumel wanda ya kai wata

ziyarar gaggawa garin na Jahun ya sha alwashin taimakawa al'umar garin da ambaliyar ta shafa.

Gameda batun tallafi dai wasu al'ummar garin na Jahun da a barama suka gamu da banner ruwa har kawo yan zu suna kokawa da cewa babu wani tallafin azo- a-gani da suka samu daga bangaren gwamnati.

kila dai a wannan karo zata sauya zani ganin girman wannan bala'i da al'ummar garin na Jahun din suke ciki.