Jonathan ya cika kwanaki dari kan mulki

Shugaba Jonathan ya cika kwanaki dari kan karagar mulki
Image caption Shugaban Najeiya,Dakta Goodluck Jonathan

A Najeriya, a yau ne shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan ke cika kwanaki dari da karbar ragamar mulkin kasar.

Shugaban kasar dai ya yi alkawarin aiwatar da wasu ayyuka don kyautata rayuwar jama`a, musamman ma inganta harkar zabe da samar da wutar lantarki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Yayin da wasu ke ganin gwamnatinsa ba ta yi wani abin a-zo-a-gani ba, jam`iyyarsa ta PDP na cewa alasambarka.

Shugaba Jonathan ya zama shugaban Najeriya ne bayan rasuwar marigayi Alhaji Umaru Musa `Yaradua a watan Mayun da ya gabata.