Yunwa na yin barazana ga dubun dubatar jama'a a Nijar

Wani jami'in kungiyar agajin nan ta Helen Keller International mai hedkwata a Amurka ya shaidawa BBC cewa a yanzu haka jama'ar kasa Nijer na cikin mummunar matsala ta karancin abinci.

Daraktan kungiyar a Afrika, Shawn Baker ya zargi kasashen duniya da gazawa wajen taimakawa Nijer.

Ya ce akwai gibin dala miliyan sittin da tara na abin da ake bukata domin taimakawa mabukata:

Mr Baker yace muddin ba a sami kudaden ba, to kuwa dubun dubatar yara za su iya rasa rayukansu.

Ya ce matsalar fari ta lalata amfanin gona da dabbobi kuma matsalar rashin abinci mai gina jiki a wasu yankunan har ta zarta kashi ashirin cikin dari na jama'ar yankunan.

Wannan kuma ya zarta abin da hukumar kiwon lafiya ta duniya za ta iya kaddamar da dokar ta baci a kai.