An soke bukin samun yancin kai a Pakistan

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

A kasar Pakistan an jingine sauran bukukuwan ranar samun mulkin kai gobe asabar face daga tutoci sama domin alhinin barnar da ambaliyar ruwa da ta rutsa da mutane miliyan goma sha hudu ta shafa.

Ana sa ran shugaba Zardari zai kwashi wunin goben yana tare da wadanda abin ya shafa a lardunan da masifar ta fi yin kamari.

Wani kakakin kungiyar agaji ta Red Cross yace miliyoyin mutane na fama da rashin tsaftataccen ruwan sha.

Ita ma majalisar dinkin duniya ta ce, an sami mutuna dubu talatin da shida dake fama da cutar gudawa a yanzu haka.