Ra'ayi Riga: Me ke hana mata shiga harkokin siyasa a kasashen Afrika?

Mata na zabe a Nijar
Image caption Mata na zabe a Nijar

A babban taron da aka yi a birnin Beijing ne a shekarar 1995, aka kulla yarjejjeniya wadda akasarin kasashen duniya suka amince za su aiwatar, inda aka bukaci warewa mata akalla kashi talatin cikin dari na mukaman da ake zaba, kamar kujerun majalissun dokoki, domin tabbatar da cewar ana damawa da su a harkokin mulki.

Sai dai kawo ya zuwa yanzu, kiddidigar da Kungiyar Majalisun dokoki ta kasashen duniya ta fitar a cikin watan Yuni, na nuni da cewar a fadin duniya baki daya, mata na da kashi goma sha tara ne kacal cikin dari na jumlar kujerun majalisun dokoki, watau kasa kenan da yarjejeniyar da aka kulla ta birnin Beijing.

Kuma koda a nahiyoyin da ake ganin harkokin siyasarsu sun samu ci gaba matuka, kasashe kalilan ne za su bugi kirji, su ce sun cika wannan alkawari.

A Kasashen Africa akwai kasashe kamarsu Rwanda da Burundi da Tanzania da Swaziland da Africa ta kudu da Angola da suka cika wannan alkawari, to amma ga saura kuwa, kamar su Nigeria, da Cameroon da Chadi, akwai sauran jan aiki, ballatana kuma Niger, inda a yanzu mulki ne irin na soji.

To shin ko me ke kawo cikas ga Mata wajen shiga harkokin siyasa, musamman a kasashenmu na Africa? Kuma wace hanya za a bi domin kara yawan matan, yadda zasu iya bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban kasa?

To domin gano dalilan da su ka sa Matan ke a cikin wannan matsayi da kuma hanyoyin da za a bi domin ganin an kara damawa da su a cikin harkokin siyasa, ina tare da wasu Mata -- da ma Maza wadanda zamu tattauna tare da su, da kuma ku masu saurarenmu.

Daga cikinsu kuwa har da Hajiya Rabi Musa Abdullahi, Jami'a a kungiyar Wrapa a Nigeria, wadda ke kula da fannin dake fafutukar ganin an dama da mata a harkokin siyasa. Akwai kuma Hajiya Na'ajatu Mohammed, wata yar siyasa a Nigeriar.

Sai kuma Dr Abdullahi Danladi Sankara, Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP, shiyyar arewa maso yammacin Nigeria. Haka kuma akwai Dr Kabir Mato, malami kan kimiyar siyasa a Jami'ar Abuja.