Tattalin arzikin Jamus ya sami cigaba

Tattalin arikin Jamus, wanda shi ne mafi karfi a Turai, ya samu cigaba mafi girma cikin watanni uku a jere, tun bayan hadewar bangarori biyu na Jamus, fiye da shekaru ashirin da suka wuce.

Tattalin arzikin ya cigaba da kashi biyu da digo 2 cikin 100, kuma hakan ya samu ne a sakamakon yawan kayyakin da kasar ke fitarwa waje da kuma irin yawan cinikayyar da aka samu a cikin gida.

Sai dai ministan tattalin arzikin Jamus din, Rainer Brue-derle ya ce akwai bukatar a kara tashi tsaye:

Ya ce: Jamus ta fita daga cikin halin tabarbarewar tattalin arziki, sai dai ba shakka har yanzu akwai bukatar daukan wasu matakai na kawo sauyi don daidaita al'ammura.

Masu aiko da rahotanni sun ce har yanzu dai baa san ko wannan cigaba ya faru ne hakan nan kawai, ko kuma mafari ne na farfadowar tattalin arzikin Turai. Galibi dai kasashe 16n dake amfani da kudin bai daya na Euro sun samu cigaban tattalin arziki, fiye da yadda aka yi zato, kuma cikin sauri fiye da Amirka.