An sace jami'an kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta duniya a yankin Darfur na Sudan ta ce an sace biyu daga cikin masu kiyaye zaman lafiyarta.

Rundunar hadin guiwar ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afrika -UNAMID -- ta ce 'yan bindiga sun kame mashawartan 'yan sanda biyu a cikin wata mota a kusa da gidansu a Nyala dake kudancin Darfur.

Wani kakakin rundunar kiyaye zaman lafiyar ya ce ba a san dalilin harin ba.

Ma'aikata 'yan kasashen waje 17 ne dai aka kame a Darfur tun cikin watan Maris na bara.

An tura rundunar ta UNAMID ne a cikin watan Janairun shekara ta dubu 2008 domin kare fararen hula da kuma inganta tsaro a Darfur.

Wakilin BBC ya ce, a halin yanzu dai rundunar kiyaye zaman lafiyar ta UNAMID tana cikin wani mawuyacin hali.

Gwamnatin Sudan na neman ta mika wasu shugabannin yankin 6 wadanda suka je wajenta domin samun kariya a sansanin Kalma, kusa da Nyala.

Ana zarginsu da tayar da fitinar da mutane da yawa suka mutu a cikinta.