Atiku ya kaddamar da neman shugaban kasa a Abuja

A Nijeriya, tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya bayyana sha'awarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin jam`iyyar PDP mai mulkin kasar.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana aniyar tasa ne a wajen wani taro a Abuja .

Ya kuwa bayyana matsayin nasa ne duk da cewa har yanzu jam`iyyar ta PDP ba tabbatar da amincewa da sake karbarsa a cikin ta ba, bayan da a baya ya bar ta zuwa jama'iyar AC.

Dubban jama`a ne dai suka halarci wajen bikin.

Sai dai manyan ya'yan jam`iyyar PDP ba su leka wajen taron ba.