Atiku Abubakar zai kaddamar da kamfe na tsayawa takara

Shugaban Jami'yyar PDP Okwesilieze
Image caption Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar zai kaddamar da neman takarar mukamin shugabankasa a wani yanayi mai sarkakiya

A Nigeria, a yau ne ake sa-ran tsohon mataimakin shugaban kasar Alh Atiku Abubakar, zai kaddamar da kamfe na neman tsayawa takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar PDP mai mulkin kasar

Atiku Abubakar din dai bai samu sahalewar uwar jam'iyyar PDP ba, kasancewar ya taba ficewa daga jam'iyyar.

Kakakin jam'iyyar PDPn, Farfesa Rufa'i Alkali ya shaidawa BBC cewa reshen jam'iyyar da ke jihar Adamawa kadai ke da hurumin baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar damar tsayawa takarar shugabancin najeriya.

To sai dai jami'an PDPn a jihar tasa ta haihuwa na cewa sam tsohon mataimakin shugabankasar bai ma koma jam'iyyar ba ballantana a yi batun takara.

Babban mai baiwa gwamnan jahar Adamawan shawara ta fuskar yada labaru, Malam Aminu Iyawa ya shaidawa BBC cewar tsohon mataimakin shugabankasar Atiku Abubkar bai bi matakan daya kamata ba wajen sake komawa jam'iyyar PDP

To sai dai tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, Alhaji Atiku Abubakar yace wannan takaddama ba zata hana shi cigaba da shirinsa na kaddamar da neman tsayawa takarar shugabancin kasar ba a karkashin jam'iyyar ta PDP.