Mutane bakwai sun mutu a Bagadaza bayan tashin hankali

Wani jerin tashe tashen hankula a ko'ina cikin Bagadaza, sun yi sanadiyar kashe mutane 7 tare da jikkata akalla 17.

An harbe wasu 'yan sunni su 3 yayinda suke barin masallaci.

'Yan sa'o'i daga bisani bama-bamai 3 da aka dana a wani muhimmin yankin kasuwanci sun kashe mutum daya da kuma raunata wasu da yawa.

An kashe wasu mutanen 3 kuma a lokacin da wani bam ya tarwatsa wata karamar bas.