Ban Ki-Moon ya kara janjantawa Pakistan kan ambaliyar ruwa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya ce daukacin duniya na tare da Pakistan bayan mummunar ambaliyar ruwan da gwamnatin Pakistan ta ce ta shafi mutane miliyan 20.

Mr Ban ya gana da Shugaba Asif Ali Zardari da kuma Firaminista Yousuf Raza Gilani, domin tattauna ayyukan bayar da agaji kafin ya tashi domin gani da kansa yankunan da lamarin ya fi kamari.

Ya bukaci kasashen duniya da su hanzarta kai dauki ga wadanda abun ya shafa.

Ya ce, ina mai farin cikin ziyartar Pakistan, amma kuma na zo nan ne a karo na biyu domin nuna jimami na da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga jama'a da gwamnatin Pakistan a wannan mawuyacin lokaci.

Haka kuma na zo nan domin bukatar kasashen duniya su hanzarta bayar da taimakonsu ga jama'ar Pakistan.

Wani wakilin BBC a Pakistan ya ce ana daukar barkewar annoba a yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa a matsayin barazana mafi girma bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da fara samun bullar ciwon kwalara.