Ana zaman makokin wadanda suka mutu a China

An rufe gidajen silima sannan an sassauto da tutoci kasa - kasa a ranar zaman makokin mutane fiye da dubu daya da dari biyu da babbar zaftarewar kasa ta halaka mako guda da ya wuce.

A wurin da bala'in ya faru, a Zhouqu cikin lardin Gansu, masu aikin ceto da mazauna garin dubu biyar sun dakatar da aiki suka kuma yi tsaye cik na tsawon mintuna uku tsit.

Mutane kusan 500 ne har yanzu ba a san yadda suka yi ba, bayan da laka ta malalo zuwa gefen tsauni a Zhouqu bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Ana dai hasashen cewar ruwan zai yi ta kwarara a cikin yan kwanaki masu zuwa.