Congo Brazzaville na bikin cika shekaru hamsin

Congo Brazzaville na bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai
Image caption Congo Brazzaville ta samu 'yancin kanta ne daga turawan mulkin mallakar kasar Faransa

A yau kasar Congo Brazzaville ke gudanar da bukukuwan cikar kasar shekaru hamsin da samun 'yancin kai daga kasar Faransa.

Dimbin shuwagabannin nahiyar Afrika ne ake sa ran za su halarci bikin cikar kasar Congo Brazzaville shekaru hamsin da samun yancin kai, kuma za'a gudanar da bikin idan an jima a yau.

A gabannin bikin dai shugaban kasar Denis Sassou Nguesso ya amince cewa kasar ta sa ba ta cigaba ba ta fannin tattalin arziki.

Congo Brazzaville na daya daga cikin kasashen Afirka masu arzikin man fetur amma kaso saba'in cikin dari na al'ummarta na rayuwane cikin kangin talauci.